News
Majalisar Dattawa Ta Bukaci Daukar Karin Sojoji 100,000 Domin Dakile Matsalar Tsaro
Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunonin sojin kasa su dauki karin jami’ai akalla 100,000, domin karfafa yaki da matsalolin tsaro da suka ta’azzara a fadin kasar.
Wannan bukatar ta biyo bayan kudirin da Sanata Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi ya gabatar, sakamakon sace dalibai 25 na makarantar sakandiren mata ta Maga da ke jihar. Sanatan ya bayyana lamarin a matsayin babban kalubale ga hukumomi, yana mai cewa hakan na iya janyo fargaba har ta kai ga dalibai mata daina zuwa makaranta.
Matar Da Ta Shirya Kashe Mijinta Kan Naira Dubu 400 Ta Faɗa Komar ’Yan Sanda A Kaduna
Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, shi ma ya nuna damuwarsa kan yawaitar garkuwa da dalibai a makarantun kasar. Majalisar ta ce ta kafa kwamiti don binciken yadda ake tafiyar da kudaden da aka ware wa shirin kare makarantu (Safe Schools Initiative).
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
