Connect with us

News

‎Tankin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutum 4, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Jigawa ‎

Published

on

FB IMG 1763554946428

‎Mutanen yankin Zugai da ke cikin Karamar Hukumar Roni a Jihar Jigawa sun wayi gari da wani mummunan ibtila’i a safiyar yau, bayan da tanki na ruwan sha da al’umma ke dogaro da shi ya karye ya fado a kan jama’a.

‎Shaidun gani da ido sun bayyana cewa tankin ya ruguje ba tare da wani alamar gargadi ba, inda ya fadi kai tsaye kan mutanen da ke tsaye suna jiran su cika kwantena domin amfanin yau da kullum. Wannan hatsari ya yi sanadin rasuwar mutane hudu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka masu tsanani.

Gwamna Abba Ya Gabatar Wa Majalisar Dokokin Kano Kasafin 2026 Na Naira Tiriyan 1 Da Biliyan 368

‎Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda suka jikkata an garzaya da su zuwa asibitin yankin domin samun kulawar gaggawa. Hakan na zuwa a yayin da al’umma ke ci gaba da nuna damuwa kan ingancin irin wadannan tankunan da ake amfani da su a karkara.

‎Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa wannan ibtila’i ya sake nuna bukatar gwamnati ta duba tsarin samar da ruwan sha, tare da tabbatar da cewa gine-ginen ruwa suna bin ka’idojin tsaro, domin kauce wa sake faruwar irin wannan hatsari a nan gaba.

 

 

Advertisement

SAWABA FM

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending