Connect with us

News

Kano: Ma’aikatar Muhalli Ta Gudanar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Tsaftar Bandaki

Published

on

IMG 20251119 WA0011

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

 

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta gudanar da gangamin tattaki na musamman domin wayar da kai kan muhimmancin tsaftar bandaki, a wani bangare na cika kudirin Majalisar Dinkin Duniya na ranar 19 ga Nuwamba, wadda aka ware domin tunatar da al’umma muhimmancin kula da tsaftar muhalli.

An gudanar da gangamin ne a safiyar ranar Laraba, 19 ga Nuwamba 2025, inda jami’an ma’aikatar suka zagaya manyan tituna da kasuwanni na birnin Kano domin fadakar da jama’a kan illolin yin bahaya a bainar jama’a.

‎Tankin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutum 4, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Jigawa ‎

Da yake jawabi madadin Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, Babban Sakataren Ma’aikatar, Barr. Mustapha Nuradeen Muhammad, ya ce manufar gangamin ita ce wayar da kai kan amfani da tsaftatattun bandakai domin rage yaduwar cututtuka da ke faruwa sakamakon rashin tsafta da kuma yin bahaya a kan tituna.

A nasa jawabin, Sarkin Tsafta na Jihar Kano, Jamilu Ahmed, ya bukaci masu hannu da shuni su samar da bandakai a kasuwanni da kusa da manyan tituna domin bai wa jama’a damar amfani da su, maimakon yin bahaya a bainar jama’a. Ya ce hakan zai taimaka matuka wajen rage yaduwar cututtuka a fadin jihar.

Advertisement

Haka zalika Sarkin Tsafta ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su daina yin bahaya a kan tituna, tare da gargadin cewa za a dauki matakin doka kan duk wanda aka kama yana aikata hakan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending