News
Fiye Da Mutane Miliyan 45 A Nijeriya Har Yanzu Suna Yin Bahaya A Waje — Gwamnatin Tarraya
Gwamnatin Tarayya ta ce matsalar rashin bandaki a Najeriya na kara ta’azzara, inda sama da miliyan 45 na ’yan kasa ke ci gaba da yin bahaya a waje.
Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ya bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai na bikin Ranar Bandaki ta Duniya ta 2025, wanda aka yi da taken “Tsabtace Muhalli a Duniyar da ke Canzawa”.
Ministan — wanda Sakataren Dindindin, Mahmud Kambari, ya wakilta — ya ce matsalar ta zama barazana ga lafiyar jama’a da muhalli, inda ya bayyana cewa kashi 25 cikin 100 na ’yan Nijeriya kawai ke da damar yin bahaya a wurare masu tsafta.
“A duniya akwai biliyan 4.2 da ba su da bandaki mai aminci. A Najeriya kuma sama da miliyan 45 har yanzu na fitar da bahaya a fili,” in ji shi.
Ministan ya nuna damuwarsa kan yadda makarantu, asibitoci da hukumomin gwamnati da dama ko dai basu da bandaki kwata-kwata ko kuma suna amfani da wadanda ba a kula da su.
Ya ce har yanzu wasu manyan birane na dogaro da tsofaffin magudanar sharar da ke gaza aiki, abin da ke janyo zubar ruwan datti zuwa koguna da rafuka — lamarin da ke iya janyo cututtuka.
Ya kara da cewa rashin tsafta na taimakawa yaduwar cututtuka kamar kwalara, gudawa, typhoid da kuma cututtukan tsutsotsi, wadanda ke kashe dubban mutane a duk shekara, musamman yara ƙasa da shekara biyar.
Ya ce wannan matsala na iya jinkirta kokarin Najeriya na cimma manufar SDG 6.2, wadda ta shafi tsaftar muhalli da ingantaccen bandaki ga kowa.
