Connect with us

News

Maganin Sauro Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar mutum 4 Yan Gida Daya A Kano

Published

on

Wata mummunar gobara ta tashi a safiyar Laraba a unguwar Kundila Layin Baba ‘Imfosibul’, da ke cikin karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a dangi ɗaya.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, ACFO Saminu Yusif, ya fitar. Ya ce jami’in hukumar, HFS Abba Datti, ne ya fara bayar da rahoton gobarar da misalin ƙarfe 4:13 na safiya.

Jirgin Ruwa Dauke Da Fasinjoji 270 Ya Yi Taho-mu-Gama A Gabar Tekun Koriya Ta Kudu

A cewar hukumar, lokacin da jami’anta suka isa wurin, gobarar ta riga ta mamaye gidan mai ɗakuna biyu, falo, kicin da bandaki.

Sanarwar ta bayyana cewa gobarar ta rutsa da mutum biyar a cikin gidan – ciki har da mahaifi mai shekaru 43, Shodandi; matarsa Rafi’a, mai shekaru 30; da ‘ya’yansu mata biyu, Mardiya (3) da Yusira (shekara 1 da rabi) – dukkansu sun mutu sakamakon shakar hayaki da konewa.

Sai dai an samu nasarar ceto yaro ɗan shekara 12, mai suna Aminu Shodandi, wanda aka fitar da shi cikin hayaniya da raunuka.

Hukumar kashe gobarar ta jajanta wa iyalan da abin ya shafa, tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da kula da wutar lantarki, tanda, da duk wasu abubuwan da ka iya haddasa gobara musamman a wannan yanayin sanyi na hunturu.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending