News
Dakarun Soji Sun Ceto Yan Mata 12 Da ISWAP Suka Sace A Borno
Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ceto yan mata 12 da mayakan ISWAP suka sace a Gundumar Mussa, Karamar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno, a cewar majiyoyin tsaro a ranar Asabar.
An sace yan matan ne ‘yan tsakanin shekara 15 zuwa 20 a ranar 23 ga Nuwamba, yayin da suke girbi a gonakin iyayensu.
Lamarin ya jawo far gaba a yankin, inda wasu mazauna suka tsere zuwa makwabtan garuruwa.
Majiyar tsaro ta bayyana wa zagazola makama cewa sojojin sun kammala aikin ceto cikin nasara, kuma dukkansu sun dawo lafiya.
Sunayen wadanda aka ceto sun hada da Fatima Shaibu (17) ,Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18), Saliha Muhammed (15), Sadiya Umaru (17), Amira Babel (15), Zara Adamu (17), Nana Shaibu (15), Zainab Musa (18), Zainab Muhammed (17), Jamila Saidu (15), Hauwa Hamidu (17)
An kai su wani wuri mai tsaro na soji domin duba lafiyarsu da yin cikakken bayaninsu kafin a mika su ga iyayensu.
Ceton ya zo ne a daidai lokacin da sojoji ke karfafa ayyukan su a kudancin Borno don murkushe ragowar mayakan ISWAP da ke da hannu a hare-hare da sace-sacen mutane.
