News
Dakarun Soji Sun Ceto Fasinjoji 21 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kogi
Jami’an tsaro a jihar Kogi sun kubutar da fasinjoji 21 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, bayan harin da aka kai kan motoci da dama a manyan hanyoyin jihar. A yayin harin, jami’an tsaro biyu — soja guda ɗaya da wani mai sa kai — sun rasa rayukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa kusan ’yan bindiga 100 ne suka tare jerin motocin fasinja, ciki har da Toyota Sienna daga Oshogbo zuwa Kaduna, Toyota Hiace daga Owo zuwa Abuja, wata Hiace daga Abuja zuwa Ekiti, da Toyota Carina daga Lokoja zuwa Kabba.
Hakanan, wata motar Dangote mai ɗauke da buhunan siminti da wata motar J5 cike da barkono daga Kano zuwa Lagos sun tsinci kansu cikin harin.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, inda fasinjoji suka shiga firgici, wasu daga cikinsu kuma aka yi ƙoƙarin yin garkuwa da su.
Rundunar haɗin gwiwa ta musamman wadda ta ƙunshi Sojojin Brigade ta 12, sashen Quick Response, jami’an NSCDC, da mafarauta da masu sa kai, ta bi ’yan bindigar cikin daji. An yi musayar wuta mai zafi, lamarin da ya kai ga ceto mutum 21 — ciki har da jaririya ’yar kwana tara a duniya.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
