News
Ƙungiyar Likitoci Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta ƙasa (NARD) ta dakatar da yajin aikin ta na ƙasa baki ɗaya bayan shafe kwanaki 29 a yajin aikin.
Dakatarwar ta biyo bayan wani taron Majalisar Zartarwar Ƙungiyar da aka gudanar a ranar Asabar, inda aka tattauna kan ci gaban da aka samu a tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.
Sakataren Ƙungiyar, Dr. Shuaibu Ibrahim, ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi ta wayar tarho, yana mai cewa an cimma matsaya bayan NARD ta sanya hannu kan takardar yarjejeniya da gwamnatin tarayya kan manyan bukatu guda bakwai da ƙungiyar ta gabatar.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
