Connect with us

News

‎Indiya Ta Cafke Yar Najeriya Da Ake Zargi Da Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi Ga Kusan mutane 2,000 A Telangana

Published

on

Dabiri Erewa

‎Hukumomin Indiya sun kama wata yar Najeriya da ake zargi da sayar da miyagun ƙwayoyi da kudinsu ya kai kusan N812m, ga mutane 1,975 a jihar Telangana.

‎Rahoton jaridar Times of India ya ce wanda ake zargin, da aka bayyana da suna Nick, tana gudanar da harkar ne ta wani dandali ta yanar Gizo ,inda ta rika tura ƙwayoyi cikin sirri cikin watanni biyu kacal.

Advertisement

‎Kamen ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani samame da jami’an Eagle Force Telangana tare da NCB, Delhi Police Crime Branch da Noida Police suka yi, inda aka kama fiye da ’yan Najeriya 50 bisa zargin tsallake biza da sauran laifuka.

Rundunar Sojin Sama Ta Tarwatsa Sansanonin Ƴan Ta’adda A Katsina Da Borno

‎A cewar rahoton, binciken da hukumar Anti-Narcotics ta Telangana ta yi ya nuna cewa ana tura buƙatun ƙwayoyi ga Nick, wanda ake zargi da kasancewa babbar mai shirya harkallar daga Najeriya.

Advertisement

‎Hukumomi sun ce ya yi amfani da lambobin waya biyu da ake sarrafawa daga ƙasashen waje, tare da gano ofisoshin tura kaya kusan 30 da take yawan amfani da su wajen aikawa da miyagun ƙwayoyi.

‎An kuma gano cewa ana amfani da kayayyakin da aka saya daga Flipkart domin ɓoye ƙwayoyi kafin a tura su, lamarin da ya fallasa hanyar sadarwar da ake amfani da ita wajen rarraba kayan.

Advertisement

 

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending