Connect with us

News

Ƴan Najeriya na neman bayani kan dala miliyan 30 na samar da tsaron makarantu

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya nemi a kara yawan kasafin kudin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.
Spread the love

’Yan Najeriya na ci gaba da neman bayani game da makomar dala miliyan 30 da aka tattara domin samar da tsaro a makarantu tun bayan sace ɗaliban Chibok a 2014, musamman ganin yadda hare-haren satar ɗalibai suka sake farfado da ƙarfi a arewacin ƙasar.

Tun bayan sace sama da ɗalibai 300 na makarantar sakandaren Chibok, hukumomin Najeriya suka kafa gidauniyar musamman don inganta tsaron makarantu, ƙarƙashin wani tsari da tsohon Firayim Ministan Birtaniya, Gordon Brown, ya tallafa masa.

Shugaba Tinubu Na Duba Yiwuwar Naɗa Janar Christopher Musa A Matsayin Sabon Ministan Tsaro

 

A shekarar 2014, hukumar kula da yankin Arewa maso Gabas ta tara naira biliyan 80, tare da gudunmawar:

Advertisement

Dala miliyan 1.5 daga ƙasar Norway

Dala miliyan 1 daga AfDB

Dala 50,000 daga shugaban bankin

Fam miliyan 1 daga gwamnatin Birtaniya

Advertisement

Bayan shekara guda kuma:

Switzerland ta bada dala miliyan 8

Amurka ta bada dala miliyan 2

Qatar ta bada dala miliyan 2

Advertisement

’Yan kasuwar Najeriya suka taimaka da dala miliyan 10

Duk da wannan tarin tallafi, satar dalibai ta ci gaba da ƙaruwa.

Binciken da jaridar The Guardian ta gudanar ya nuna cewa a cikin ’yan shekarun nan, an kai wa makarantu hari 20 a jihohi 10 na arewacin Najeriya, lamarin da ya haifar da:

Sace ɗalibai sama da 2,000

Advertisement

Rufe makarantu kusan 800

Kungiyar Save the Children ta ce har yanzu makarantun yankin na fuskantar barazana ta tsaro.

Babbar jami’ar da ke kula da shirin tsaron makarantu, Hajiya Halima Iliya, ta bayyana cewa gwamnati ta amince da sabon shiri na shekaru uku (2023–2026) domin gyara tsaron makarantu.

A cewar ta, za a kashe:

Advertisement

Naira biliyan 32.58 – 2023

Naira biliyan 36.98 – 2024

Naira biliyan 37.15 – 2025

Naira biliyan 38.03 – 2026

Advertisement

Ta ce shirin zai gudana ne a makarantu 48 a kowace jiha daga cikin jihohi 18 da suka fi fama da matsalar tsaro.

Kididdiga ta nuna cewa makarantu sama da 42,000 za su ci gajiyar shirin, musamman wajen samar da katange da kayan tsaro.

Sai dai har yanzu akwai makarantun sakandare 4,270 a jihohin arewa 19 da biyu a kudu da ba su da katanga.

Ga adadin jihohin da ke da mafi yawan makarantun da ke buƙatar katanga:

Advertisement

Bauchi – 574

Benue – 447

Kano – 500

Adamawa – 379

Advertisement

Jigawa – 269

Sauran jihohin sun haɗa da:

Kogi – 296

Kebbi – 203

Advertisement

Kaduna – 164

Filato – 159

Gombe – 161

Katsina – 145

Advertisement

 

FRI HAUSA.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *