News
Hukumar CAC Za Ta Fara Kama Masu POS Da Basu Yi Rijista Ba Daga Sabuwar Shekara
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su.
A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN).
Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar.
Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan Najeriya, ciki har da ’yan kasuwa ƙanana da masu aiki a karkara, cikin haɗarin tattalin arziki da asarar jari.
“Duk fintech da ke ba da damar ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba za a saka su cikin jerin waɗanda ake sa wa ido, sannan za a kai rahotonsu ga CBN. Duk masu PoS an umurce su da su yi rajista nan da nan. Bin doka wajibi ne.
“Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ba wani mai PoS da zai ci gaba da aiki a Najeriya ba tare da cikakken rajista ba,” in ji CAC.
Wannan daiba shi ne karo na farko da aka yi kira kan buƙatar tsaurara dokokin sa ido kan harkar PoS ba.
An sha yin kira ga CBN da ya ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile yawaitar damfara da ke addabar harkar PoS a faɗin ƙasar.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News13 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
