News
Mutum 4 Sun Rasu Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum uku bayan sun faɗa rijiya a ƙaramar hukumar Bichi. Duk da kokarin da jami’an ceto suka yi, an ce an ciro su ne ba su da rai.
Haka kuma, wani yaro ya rasu bayan ya faɗa rijiya a ƙaramar hukumar Danbatta. Hukumar ta ce ta samu kiran gaggawa, amma kafin a kai ga ceton shi, ruwan rijiya ya yi mummunar tasiri a jikinsa.
Manyan Ƙasashen Waje Ne Suke Taimaka Wa ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda A Najeriya —Sheik Gumi
Hukumar kashe gobara ta Kano ta ce tana ci gaba da wayar da kai ga jama’a kan kula da masauki, tsaftar muhalli da kuma rufe rijiyoyi da kyau domin kauce wa irin waɗannan hadurra masu ci gaba da faruwa a ƙananan hukumomi daban-daban na jihar.
A wani lamari daban da ya faru Hukumar tabbatar da cewa wata yarinya mai shekaru goma ta rasu a sakamakon gobarar da ta tashi a layin Day By Day da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a ranar Juma’a.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce gobarar ta tashi ne a cikin wani gida, inda wutar ta yi mummunar barna kafin jami’an hukumar su isa wurin. Ya ce yarinyar ta rasa rayuwarta ne a lokacin da ake ƙoƙarin ceton ta.
