News
Wani Dattijo Mai Shekara 65 Tare Da Ɗansa Sun Mutu A Cikin Rijiya A Kano
Mutane uku ne suka rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.
A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo.
Hukumar CAC Za Ta Fara Kama Masu POS Da Basu Yi Rijista Ba Daga Sabuwar Shekara
Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take ƙasa ta koma kan dattijon mai shekara 65 da ke haƙar rijiyar.
Hakan ya sa ɗansa mai shekara 20 shiga rijiyar domin fito da shi amma abu ya tura.
A nan ne na ukunsu mai 60 Yakubu Abdullahi shi ma ya shiga domin ceto su, amma duka dai abu ya gagara.
A ƙarshe jami’an Hukumar Kashe Gobara sun yi nasarar ceto su ukun a sume, amma daga baya likita ya tabbatar da rasuwarsu bayan kai su asibiti kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana.
