News
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin
Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi.
Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar.
Gwamnatin Taraba Ta Sassauta Dokar Taƙaita Zirga-zirga A Wasu Yankunan Jihar
Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa.
Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu labarin halin da Shugaba Talon masi shekara 67, wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki.
Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma sojoji na neman shawo kan lamarin.
Ofishin Shugaban Kasar ya sanar cewa Shugaba Talon yana cikin koshin lafiiya, kuma sojojin kasar na kokarin murkushe wasu ‘yan tsiraru da ke yunkurin juyin mulkin.
