Connect with us

News

Kano: An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Ƙara Kaimi Wajen Samar da Kayan Koyo a Makarantar Kurame ta Wudil

Published

on

IMG 20251208 WA0004
Spread the love

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ƙara dagewa wajen samar da kujeru da sauran kayan koyo da koyarwa a Makarantar Kurame da ke karamar hukumar Wudil.

Shugaban makarantar, Malam Badamasi Ibrahim, ne ya bayyana haka lokacin da kungiyar PLAN International ta ziyarci makarantar domin tunawa da Ranar Masu Bukata ta Musamman ta Duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware a kowace shekara.

Gazawar Gwamnatin Tarayya Ne, Jihohi Su Dauki ‘Yan Sa Kai A Matsayin Jami’an Tsaro Ba Tare Da Horo — Kwankwaso 

Malam Badamasi ya ce makarantar na fuskantar matsalar ƙarancin kujeru, kayan aiki da kuma littattafan koyon masu nakasar ji, yana mai rokon gwamnati da masu hannu da shuni su mara wa makarantar baya.

Advertisement

Shi ma a nasa jawabin, Jose Suru, mai kula da sashen Masu Bukata ta Musamman na PLAN International, ya ce ziyarar ta yi nufin duba halin da daliban ke ciki tare da isar musu da tallafin kayan karatu da kayan aikin da suka dace da su.

A nasa bangaren kuma, Engr. Abdulrazak Zango, shugaban kungiyar Gamayya Masu Neman Mafita ga Rayuwar Masu Bukata ta Musamman, wanda shi ma na fama da matsalar gani, ya shawarci daliban su dage da karatu, domin ilimi shi ne ginshikin ci gaban duk wani ɗan Adam.

A ƙarshe, wakiliyar mu Safiya Muhammad Usman ta rawaito cewa shugaban Ma’aikatar Ilimi na karamar Hukumar Wudil, Ibrahim Idris Indabo, ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka zabi makarantar domin ƙarfafa gwiwar ɗaliban da kuma inganta samun ilimi na musamman domin kyakkyawar makoma.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *