News
Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Kano
Wani jirgin sama mai zaman kansa mallakin kamfanin Flybird ya yi saukar gaggawa a safiyar Lahadi a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), bayan tasuwar sa daga Abuja.
Majiyoyi sun shaida wa Solacebase cewa jirgin, wanda ke ɗauke da mutane 11 ciki har da ma’aikatan jirgi uku, ya gamu da matsala ne yayin sauka da misalin karfe 9:30 na safe, lamarin da ya tilasta yin saukar gaggawa.
Wani shaidar gani-da-ido ya ce an samu nasarar fitar da dukkan fasinjojin lafiya, ba tare da rahoton asarar rai ko munanan raunuka ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan batun tsaron zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya, biyo bayan wasu makamantan abubuwa da suka faru a baya-bayan nan.
— Karin bayani na nan tafe.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
