Connect with us

News

Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado Ya Kaddamar Da Aikin Gina Katafariyar Gadar Kogin Karofin Yashi

Published

on

IMG 20251214 WA0009

A wani yunkuri na inganta hanyoyin zirga-zirga da rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta, zababben Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili, ya kaddamar da aikin gina katafariyar gadar Kogin Karofin Yashi, wadda za ta haɗa Mazabar Karofin Yashi da Tamawa.

An kaddamar da aikin ne a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2025, a gaban manyan jami’an karamar hukumar da al’ummar yankin, inda aka bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki na warware matsalar da kogin Karofin Yashi ke haifarwa, musamman a lokutan damina.

Advertisement

Shugaban NUJ Na Ƙasa Ya Jagoranci Buɗe Ofishin Kano Online Media Chapel, Yayi Alƙawarin Inganta Walwalar Ƴan Jarida

Gadar, wadda ake sa ran za ta inganta zirga-zirga, ta daɗe tana zama babban cikas ga harkokin kasuwanci, ilimi da sauran muhimman ayyukan yau da kullum, lamarin da ke jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali a duk lokacin da ruwa ya cika kogin.

Da yake jawabi yayin taron, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili ya ce ginin gadar na daga cikin manyan alkawuran da ya ɗauka wa al’ummar Rimin Gado, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar magance matsalolin da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

Advertisement

“Gadar Karofin Yashi ta daɗe tana ci wa al’umma tuwo a kwarya, amma a yau mun fara kawo ƙarshen wannan matsala,” in ji shi.

Shi ma a nasa jawabin, Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Rimin Gado, Alhaji Sale Adamu, ya bayyana cewa aikin gadar zai taimaka wajen haɗa al’umma, bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙarfafa tsaro a yankin, yana mai yabawa shugabancin karamar hukumar bisa hangen nesa da fifita ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga jama’a.

Advertisement

Al’ummar Karofin Yashi da Tamawa sun nuna matuƙar farin ciki da godiya bisa kaddamar da aikin, inda suka bayyana gadar a matsayin “ceton rai” da zai rage musu wahalhalun da suka shafe shekaru suna fuskanta.

An kammala taron ne da addu’o’in neman Allah Ya ba da nasarar kammala aikin cikin inganci da lokaci, tare da sanya albarka da zaman lafiya a Karamar Hukumar Rimin Gado baki ɗaya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending