Connect with us

News

Jami’an EFCC Sun Kama Wasu Bokaye Da Dala Miliyan 3.4 Da €280,000 Na Jabu A Osun Da Lagos

Published

on

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC reshin Ibadan sun kama wasu bokaye biyar a Jihohin Osun da Legas bisa mallakar makudan kuɗaɗen ƙasashen waje na jabu da suka kai dala miliyan 3.43 miliyan da yuro €280,000.

An kama waɗanda ake zargin ne bisa zargin zambatar wata mata mai suna Halima Sanni naira miliyan 26.55, da sunan zummar warware mata matsalolinta da tsarkake ta.

Shugaba Tinubu Ya Soke Ƙarin Girma Har Ninki Biyu Da Ya Yi Wa Dogarinsa

Waɗanda aka kama sun hada da maza biyu da mata uku, kuma an kama su ne a wuraren ibadarsu da ke Jihohin Osun da Legas bayan ayyukan leƙen asiri da EFCC ta jagoranta.

A cewar binciken, wadanda ake zargin suna fakon wadanda ba a san ko su waye ba ta hanyar da’awar cewa suna bayar da magunguna na ruhaniya ga cututtuka daban-daban da kalubalen rayuwa.

An kuma ce sun yaudari wadanda ake zargin da ikirarin suna da rauhanan da za su samar da makuɗan kuɗaɗen kasashen waje, wanda, a cewarsu, yana bukatar tsarkakewar ruhaniya daga wani aljani kafin a kashe kudin.

Masu binciken EFCC sun bayyana cewa ana yaudarar mutanen da cewa sai sun kawo nasu kuɗaɗen, wajen aiwatar da wancan aikin na tsarkakewar.

Advertisement

Baya ga jabun kudaden kasashen waje, jami’an sun kwato motoci biyu na alfarma da wasu wayoyin hannu daga wadanda ake zargin a lokacin aikin.

Hukumar EFCC ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending