Connect with us

News

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki A Ingila

Published

on

doctors (1)
  1. Sakataren lafiya na Birtaniya, Wes Streeting, ya nemi afuwar marasa lafiya yayin da likitoci a Ingila suka fara yajin aiki na kwanaki biyar kan rashin albashi mai gwabi da yanayin aiki.

Streeting ya ce gwamnati ta yi kokari matuka domin hana yajin aikin, ciki har da tattaunawar karshe da kungiyar likitoci ta BMA, amma ba a cimma matsaya ba. Ya yi gargadin cewa yajin aikin ya zo ne a wani lokaci mai matukar wahala ga hukumar lafiya ta NHS, yayin da asibitoci ke fuskantar karuwar mura da sauran cututtukan wannan yanayi na sanyi da ake ciki a nahiyar Turai.

Trump Ya Saka Najeriya Da Ƙasashen Afirka 4 Cikin Jerin Da Ya Haramta Wa Shiga Amurka

Gwamnatin ta ce likitocin sun riga sun samu karin albashi kusan kashi 29 cikin 100, kuma ana bude kofar tattaunawa kan shekaru masu zuwa. Sai dai likitocin sun ce hakan bai wadatar ba.

Kungiyar BMA ta ce dole ne gwamnati ta fito da tsari mai dorewa kan albashi da samar da sabbin ayyukan yi domin kauce wa karin yajin aiki.

Yajin aikin ya fara ne da safiyar Laraba, kuma shi ne yajin aiki na 14 da likitocin Ingila suka shiga tun shekarar 2023.

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending