Connect with us

News

Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa NIN Ta Zama Lambar Haraji Ga Duk ’Yan Najeriya – FIRS

Published

on

FB IMG 1766492943456

Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta tabbatar da cewa Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da Hukumar Kula da Shaidar Ƙasa (NIMC) ke bayarwa, yanzu ita ce lambar tantance haraji (Tax Identification Number) ga dukkan ’yan Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani shiri na wayar da kan jama’a kan sabbin dokokin haraji, inda ta wallafa bayanin a shafinta na X (tsohon Twitter).

Advertisement

FRSC Ta Tura Ƙarin Jami’ai Kan Hanyar Abuja–Lokoja Bayan Cunkoson Motoci Na Kwanaki Biyu

A cewar FIRS, ba sai ɗan ƙasa ya nemi wata sabuwar lambar haraji ba, domin NIN ɗinsa ta riga ta zama lambar harajinsa kai tsaye a ƙarƙashin sabon tsarin.

Haka kuma, hukumar ta ce kamfanoni da aka yi wa rijista ba za su ƙara neman wata lambar haraji ta daban ba, domin lambar rajistar su ta Hukumar Kula da Kamfanoni (CAC) za ta riƙa aiki a matsayin lambar harajin su.

Advertisement

Bayyanar wannan matsayi na zuwa ne bayan da wasu ’yan ƙasa suka nuna damuwa kan sabbin dokokin haraji, musamman waɗanda ke buƙatar gabatar da lambar haraji wajen wasu muhimman mu’amaloli, ciki har da buɗe ko mallakar asusun banki.

FIRS ta bayyana cewa Dokar Gudanar da Haraji ta Ƙasa (NTAA), wadda za ta fara aiki daga Janairu 2026, ta tanadi amfani da lambar haraji a wasu muhimman harkoki na kuɗi da kasuwanci.

Advertisement

Sai dai hukumar ta jaddada cewa ba sabon tsari ba ne, domin tun daga shekarar 2019 ake amfani da shi, sai dai yanzu aka ƙara ƙarfafa aiwatarwa da haɗa tsarin gaba ɗaya.

FIRS ta ƙara da cewa sabon tsarin zai haɗa dukkan lambobin haraji da ake amfani da su a baya zuwa guda ɗaya, domin sauƙaƙa tantance masu biyan haraji, hana maimaituwar biyan haraji, rage satar haraji, da tabbatar da adalci a tsarin tattara haraji.

Advertisement

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jita, tana mai cewa sabbin dokokin harajin an tsara su ne domin sauƙi, gaskiya da inganta tattara haraji a faɗin ƙasar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending