News
Yadda Wani Matashi Ya Yi Ajalin Ɗan’uwansa Kan Bashin Naira 4,000
Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lekan Lasisi, bisa zargin kashe ɗan’uwansa bayan rikici da ya ɓarke tsakaninsu kan bashin Naira 4,000.
Lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Disamba, 2025, a unguwar Abule Tuntun da ke ƙaramar hukumar Odeda, a cewar majiyoyi daga ’yan sanda.
Yadda Wasu Hasalallun Matasa Suka Babbake Ofishin NSCDC A Kano
Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga yawan basussukan da marigayin , lamarin da ya jefa iyalin cikin matsin lamba musamman bayan da masu bin bashi ke neman wanda ake zargin ya biya bashin a madadin ɗan uwansa.
A cewar Lasisi, rikicin ya ƙara tsananta ne bayan wata mata ta sake kai ƙara a kansa kan bashin Naira 4,000 da take bin marigayin, bayan dawowarsa daga kasuwa.
Ya ce yayin da yake magana da ɗan uwansa kan halin bin bashi, sai marigayin ya fusata tare da ɗauko adda, abin da ya sa shi ma ya fito da bindiga, kasancewarsa mafarauci.
Inda ya ce bindigar ya harba ta ne ba tare da niyya ba, harsashin kuma ya samu ɗan’uwansa wanda daga bisani ya rasu
“Ban yi niyyar kashe shi ba, bindigar ce kawai ta tashi ba zato ba tsammani,” in ji shi yayin amsa tambayoyi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta ce an tura lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Eleweran, domin ci gaba da bincike
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
