News
’Yan Sanda Sun Dakatar Da Fara Kamen Motoci Masu Gilashi Mai Duhu A Najeriya
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da jingine fara aiwatar da kamen motocin da ke da gilashi mai duhu ba tare da lasisi ba a fadin ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya fitar a Ranar Alhamis
A cewar sanarwar, rundunar ta dakatar da fara kamen ne wanda aka shirya fara shi daga gobe Juma’a, 2 ga watan Janairu, sakamakon umarnin kotu da ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Janairu.
Dakarun Sojin Sama Sun Yi Nasarar Hallaka Ƴan Ta’adda Dubu 2 Da 351 A 2025
Tun da farko, rundunar ’yan sandan ta sanar da cewa za ta fara kama motocin da ke amfani da gilashi mai duhu ba tare da ingantaccen lasisi ba, matakin da ta ce yana da nufin ƙarfafa tsaro da bin doka a ƙasar.
Sai dai bayan shigar da ƙara a gaban kotu kan batun, alkalin kotun ya bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar har zuwa ranar da za a sake sauraron shari’ar.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta ci gaba da bin umarnin kotu tare da sanar da al’umma duk wani sabon mataki da ya shafi batun nan gaba.
