Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Yi Barin Wuta Tare Da Hallaka Mutane Da Dama A Wata Kasuwa A Neja

Published

on

IMG 20260104 WA0005
Spread the love

‎’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 30 a kasuwa, ciki har da ƙananan yara da mata Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

‎Maharan sun yi wa ’yan kasuwar kisan gilla ne a Kasuwar Daji da ke yankin Demo inda suka yi awon gaba da tarin kayan abinci da sauran kayayyaki masu darajar miliyoyin naira, sannan suka banka wa kasuwar wuta.

Mutane 20 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Kifewar Wani Jirgin Ruwa A Nguru

‎Shaidu sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun mamaye yankin ne da misalin ƙarfe 4 na yamma a ranar Asabar, inda suka ci gaba da aikata ta’addanci har zuwa safiyar Lahadi ba tare da wani kalubalantar su ba.

AMINIYA  ta ruwaito cewa ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba tukuna.

Advertisement

‎Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa sama da mutum 50 aka ɗaure sannan aka yanka su ba tare da tsangwama ba.

‎Rahotanni sun ce dandazon maharan sun fito ne daga National Park da ke Ƙaramar Hukumar Borgu.

‎Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce sama da mutum 30 sun mutu yayin da wasu da dama aka yi garkuwa da su.

‎A cewarsa: “A ranar Asabar da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, ’yan bindiga daga dajin National Park da ke Gundumar Kabe sun mamaye Kasuwan Daji da ke kauyen Demo, suka ƙone kasuwa, suka fasa shaguna, suka kwashe kayan abinci.

Advertisement

‎“An tabbatar da mutuwar fiye da mutum 30 a harin. An kuma yi garkuwa da wasu.

‎“A halin yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kuma za a ci gaba da sanar da ci-gaban lamarin.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *