Connect with us

News

Mutane 20 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Kifewar Wani Jirgin Ruwa A Nguru

Published

on

01000000 0aff 0242 4293 08dcba79441c w408 r1 s
Spread the love

Mutane 20 sun rasa rayukansu yayin da aka ceto 13 da rai sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da ya tashi daga Adiyani a Karamar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa zuwa Nguru a Jihar Yobe.

‎Wani mazaunin garin Nguru ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da neman wasu mutane 15 da ake zargin sun nutse cikin ruwan, yayin da jami’an ceto ke gudanar da ayyukan ceto da bincike a yankin.

Kungiyar Mashawartan Gwamnan Kano Ta Bukaci Yan Siyasa Su Guji Kalaman Da Ka Iya Tayar Da Rikici Ko Haddasa Rarrabuwar Kai A Jihar

‎Hatsarin, wanda ya faru da misalin karfe 7 na daren Asabar, ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, yayin da mazauna ke bai wa jami’an ceto goyon baya a kokarin gano sauran mutanen da ake fatan ceto ko gano gawarwaki.

Rahotanni na nuni da cewa ‎Mazauna yankin sun ce suna cikin damuwa da rashin tabbas game da wasu ‘yan uwansu da ke cikin jirgin, yayin da hukumomi suka yi kira ga jama’a da su kiyaye hanyoyin ruwa da bin ka’idojin tsaro.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *