News
Gargaɗi: Shan Magani Ba Tare Da Izinin Likita Ba Na Iya Janyo Mummunar Illa Ga Lafiya – Masana
Mutane da dama a Najeriya na shan magunguna kai tsaye daga shagunan sayar da magani ba tare da izinin likita ba, lamarin da masana ke cewa na ƙara zama ruwan dare a birane da ƙauyuka.
Wasu daga cikin jama’ar na danganta hakan da sauƙin samun magani a kanti, rahusarsa, da kuma saurin biyan buƙata idan aka kwatanta da zuwa asibiti.
A wasu lokuta kuma, tsadar kuɗin asibiti, ƙarancin lokaci, da guje wa cunkoso a cibiyoyin lafiya na taka rawa.
Sai dai ƙwararru sun gargaɗi cewa wannan ɗabi’a, duk da cewa tana iya ba da sauƙi na ɗan lokaci, na iya janyo barazana ga lafiyar mutum.
Da take magana da BBC, Dr. Amina Abdullahi ta bayyana cewa shan magani ba tare da cikakken binciken likita ba na iya haddasa matsaloli masu tsanani.
Ta ce amfani da magunguna ba bisa ƙa’ida ba na iya lalata hanta, wadda ke da alhakin tace magunguna a jiki. “Idan aka riƙa shan magani fiye da ƙima, hanta na iya gajiya ta kasa aiki,” in ji ta.
Likitar ta kuma yi gargaɗi kan lalacewar ƙoda, inda ta ce wasu magunguna, musamman masu rage jin zafi da na gargajiya, na iya haddasa gazawar ƙoda.
A cewarta, shan wasu magunguna ba tare da kulawa ba na iya haifar da ulcer ko zubar jini a hanji, musamman idan an sha su na dogon lokaci.
Dr. Amina ta ƙara da cewa wasu magunguna kan haddasa rashin daidaiton jini, wanda zai iya jawo jiri, faɗuwa ko bugun zuciya, musamman ga masu hawan jini ko cututtukan zuciya.
Ta kuma yi nuni da cewa shan magani ba tare da gano asalin cuta ba na iya sa cuta ta ƙara tsananta, tare da jinkirta warkewa ko haifar da matsaloli na dogon lokaci.
Likitar ta ce alamomi irin su ciwon ƙirji, zazzaɓi mai tsanani, fitar jini ko matsanancin ciwon ciki, ba su dace a rika magance su ta hanyar sayen magani kai tsaye daga kanti ba.
A ƙarshe, ta shawarci jama’a da su rika zuwa asibiti domin a tantance lafiyarsu yadda ya kamata kafin amfani da kowanne irin magani.
