News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Da Wasu Mutane 5 A Kano
Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta kama wani da ake zargin yana dillancin miyagun ƙwayoyi tare da wasu mutum biyar da ake zargin ƴan daba ne, a wani sumame da ya kai ga ƙwato miyagun ƙwayoyi da makamai masu haɗari a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce jami’an ƴansanda na Jaoji ne suka aiwatar da kamen a ranar 10 ga Janairu, 2026, a wani ɓangare na ƙoƙarin rundunar na yaƙar safarar miyagun ƙwayoyi da laifuka masu alaƙa da su.
Rundunar ta bayyana cewa wanda ake zargin dillalin ƙwayoyi, Hafizu Ali mai shekaru 25, mazaunin unguwar Jaoji, an kama shi ne tare da wasu mutum biyar da aka bayyana a matsayin ragowar ƴan daba da aka tarwatsa. A lokacin sumamen, an same shi da ƙwayoyin Pregabalin guda 2,070 da kuma fakiti 23 na tabar wiwi da ake zargi.
Baya ga haka, rundunar ta ce an kuma ƙwato wuƙaƙe guda huɗu, da almakashi biyu da gatari guda ɗaya daga hannun waɗanda ake zargi. Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’ummar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa rundunar, yayin da ya tabbatar da cewa ana ci gaba da yin bincike kafin gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu.
