News
An Tafi Da Malam Ibrahim Isah Makwarari Gidan Yari Saboda Rashin Cika Sharuɗan Beli
Kotun Majistare da ke zamanta a Kano ta ba Malam Ibrahim Isa Makwarari beli kan kuɗi Naira miliyan 20, bayan gurfanar da shi bisa zargin mallakar takardun filaye na bogi.
Kotun ta sanya sharuɗɗa masu tsauri kafin sakin wanda ake tuhumar, inda ta umurce shi da gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.
Jami’an ‘Ƴansanda Sun Tabbatar Da Sace Mutane Sama Da 160 A Kaduna
A cewar sharuɗɗan belin, mutum na farko dole ne ya kasance dagaci ko limamin masallaci a cikin ƙaramar hukumar da yake, tare da gabatar da takardar naɗinsa daga masarauta. Mutum na biyu kuma dole ne ya kasance fitaccen mutum a jihar Kano mai gida na kansa, wanda ke da takardar shaidar mallaka (C of O) da darajarta ta haura Naira miliyan 50.
Haka kuma, kotun ta umarci Makwarari da ya miƙa fasfonsa na tafiye-tafiye ga kotu, kuma ba zai karɓe shi ba har sai an kammala shari’ar.
Zargin da ake masa
Arewa Updates ta ruwaito cewa ana zargin Malam Ibrahim Isa Makwarari da mallakar takardun filaye guda biyu da ake zargin na bogi ne, waɗanda ke ɗauke da sunayen Alƙasim Usman Baba da Audu Danyaro Fagge.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban 2025 ne kotu ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan ƙarar da Ma’aikatar Kasa ta Jihar Kano ta shigar, dangane da wani fili da ke kan titin Ahmadu Bello Way a Kano.
A yayin binciken, jami’an tsaro sun ce sun samu wanda ake tuhuma da waɗannan takardun, amma bai gamsar da su da hujjoji kan sahihancinsu ba.
Bayan karanta masa tuhumar, Malam Ibrahim Isa Makwarari ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.
Ra’ayoyin ɓangarorin biyu
Lauyan wanda ake tuhumar, Barista A. T. Shehu, ya roƙi kotu ta ba da belin abokin aikinsa, yana mai cewa zai gabatar da mutane sahihai da za su tsaya masa.
Sai dai mai gabatar da ƙara daga ɓangaren gwamnati, Barista Nura A. Salisu, ya nuna adawa da bayar da belin, yana mai cewa tun watan Oktoban bara ake neman wanda ake tuhumar, amma ya ƙi amsa gayyatar ’yan sanda har sai da aka kama shi da umarnin kotu.
Ya roƙi kotu da ta sanya tsauraran sharuɗɗa idan za a ba da belin.
Ranar dawowa kotu
Daga ƙarshe, kotun ta amince da bayar da belin Makwarari kan Naira miliyan 20 tare da cika dukkan sharuɗɗan da ta gindaya.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, 2026 domin ci gaba da shari’ar.
