Connect with us

News

Sojoji 16 Na Fuskantar Shari’a Kan Zargin Yunƙurin Juyin Mulki — DHQ

Published

on

ezgif.com gif maker

Shalkwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da cewa an yi yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar da ta gabata, bayan kammala bincike mai zurfi kan wasu jami’an soji da ake zargi da hannu a lamarin.

A cewar shalkwatar tsaron, yunƙurin juyin mulkin ya faru ne a watan Oktoban 2025, inda binciken cikin gida da rundunar soji ta gudanar ya gano cewa wasu jami’an tsaro sun kitsa shirin ne a ɓoye, kafin daga bisani a gano tare da dakile shi..

Advertisement

Jami’an ’Yan Sanda Sun Daƙile Yunƙurin Fashi Da Makami A Abuja

Tun a wancan lokaci, DHQ ta sanar da kame jami’an soji 16 masu mukamai daban-daban, daga kyaftin zuwa Birgediya Janar, bisa zargin saɓa dokokin aikin soja. Sai dai a lokacin, rundunar sojin ta musanta cewa kamun yana da alaƙa da yunƙurin kifar da gwamnati.

Advertisement

Duk da hakan, wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa sashen tattara bayanan sirri na ƙasa ne ya gano wani taron sirri da jami’an ke gudanarwa dangane da shirin juyin mulki, lamarin da ya sa aka ɗauki matakin gaggawa.

A wancan lokaci kuma, an alaƙanta soke bikin faretin Ranar Ƙasa ta 1 ga Oktoba da wannan yunƙuri, sai dai daraktan yaɗa labarai na DHQ, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya yi watsi da rahoton, yana mai bayyana shi a matsayin ƙoƙarin haddasa firgici da ruɗani a tsakanin jama’a.

Advertisement

Sai dai a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Manjo Janar Sama’ila Uba ya ce bayan kammala bincike mai tsanani irin na soja, an tabbatar da cewa jami’an da aka kama sun kitsa shirin kifar da gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Manjo Janar Uba ya ƙara da cewa jami’an za su gurfana a gaban kotun soja domin amsa tuhumar da ake yi musu, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da shari’ar ne bisa ƙa’idojin gaskiya, adalci da tanadin dokokin aikin soja na Najeriya.

Advertisement

Shalkwatar tsaron ta jaddada aniyarta na kare dimokuraɗiyya da tsarin mulkin ƙasa, tare da yin gargaɗi kan duk wani yunƙuri da ka iya zama barazana ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending