News
Kashi 58% Na Mata Masu Juna Biyu A Najeriya Na Fama Da Ƙarancin Jini – Gwamnatin Tarraya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce kashi 58 cikin 100 na mata masu juna biyu a ƙasar na fama da matsalar ƙarancin jini a jiki, lamarin da ta danganta da rashin cin abinci mai wadataccen sinadaran gina jiki.
Shugabar sashen kimiyyar gina jiki a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Helen Achimugu, ce ta bayyana hakan a Abuja, yayin wani taron horas da manema labarai da ƙungiyar Civil Society–Scaling Up Nutrition in Nigeria (CS-SUNN) ta shirya.
Gwamnatin Borno Ta Karɓi ‘Yan Gudun Hijira 300 Da Suka Dawo Gida Daga Kamaru
Ta ce sakamakon binciken NDHS na shekarar 2023 ya nuna cewa kusan rabin adadin mata masu haihuwa a Najeriya na fama da ƙarancin jini, matsalar da ke barazana ga lafiyar mata da jarirai.
Achimugu ta bayyana cewa matsalar na shafar yara ƙanana matuƙa, inda ta ce Najeriya ce ta farko a Afirka, kuma ta biyu a duniya, wajen yawan yaran da ba sa girma yadda ya kamata.
“Akwai yara miliyan 35 da ke fama da rashin girman jiki, miliyan 14 da ke fama da rama, sannan miliyan 24 na fama da ƙarancin jini,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa ana kiran matsalar da suna “boyayyar yunwa”, saboda ba a cika ganin alamunta kai tsaye ba, sai dai ta bayyana ta hanyar raunin jiki, raguwar kaifin basira da gajiya.
A cewarta, rashin samun sinadaran gina jiki kamar iron, iodine, zinc, folate da vitamin A ne ke haddasa matsaloli irin su rama, rashin girma yadda ya kamata da raunin kwakwalwa, musamman a tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekara biyar da mata masu juna biyu.
Ta ce matsalar ta fi yaduwa a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin abinci, musamman a Arewacin Najeriya.
Dangane da matakan da gwamnati ke ɗauka, Achimugu ta ce ana wayar da kan jama’a kan muhimmancin abinci mai gina jiki, tare da rarraba maganin Multiple Micronutrient Supplements (MMS) ga mata masu juna biyu.
Ta bayyana cewa kwalba ɗaya ta MMS na wadatar mace tsawon watanni shida, kuma na taimakawa wajen rage haɗarin zubar jini a lokacin ciki da haihuwa.
Taron ya samu halartar manema labarai 39 daga jihohin Kano, Kaduna, Lagos, Bauchi, Niger, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya Abuja.
A nasa jawabin, Shugaban CS-SUNN, Sunday Okoronkwo, ya buƙaci manema labarai da su taka rawar gani wajen wayar da kan al’umma kan illolin ƙarancin jini, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalar musamman a tsakanin mata da yara ƙanana.
