News
Rikicin Masarautar Kano Zai Zo Ƙarshe Ba Da Jimawa Ba —Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa rikicin da ya daɗe yana kewaye da masarautar Kano zai zo ƙarshe ba da jimawa ba, yayin da take ɗaukar matakai domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar laraba.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta riga ta fara aiwatar da wasu tsare-tsare na musamman da nufin warware rikicin masarautar, tare da tabbatar da cewa lamarin ba zai ci gaba da janyo tashin hankali ko kawo cikas ga harkokin mulki ba.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake naɗa Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16 a watan Mayun 2024, bayan tsige Aminu Ado Bayero daga karagar mulki.
Naɗin ya biyo bayan rattaba hannu da gwamnan ya yi kan dokar Kano State Emirate Council (Repeal) Law 2024, wacce ta soke dokar masarautu ta shekarar 2019, tare da rusa masarautun da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki, yana mai jaddada cewa an gina tsarin warware rikicin ne bisa mutunta doka, darajar masarautu da kuma muradun al’ummar Kano.
Dangane da sauya sheƙar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC, Waiya ya bayyana matakin a matsayin wanda zai kawo alheri ga jihar Kano.
Ya ce kusantar da jihar za ta yi da Gwamnatin Tarayya zai taimaka wajen jawo ƙarin ayyukan raya ƙasa da tsoma bakin ci gaba, musamman a fannoni kamar gine-gine, lafiya, ilimi da walwalar jama’a.
Da yake tsokaci kan makomar mataimakin gwamnan jihar, wanda bai sauya sheƙa tare da gwamnan ba, Kwamishinan ya ce hakan lamari ne na ra’ayin kansa, yana da ’yancin zaɓar inda zai tsaya a sabuwar tafiyar siyasar.
