News
’Yan Ta’adda Sun Ƙone Mutane Da Ransu A Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ’yan ta’adda sun kashe tare da ƙona mutane huɗu da ransu a ƙauyen Gwargwabe, da ke yankin Nahuce a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta jihar.
Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, kafin sallar Magriba, lokacin da ’yan ta’addan suka shiga ƙauyen, suka ƙona gidaje da rumbunan abinci, tare da hallaka maza uku da mace ɗaya, baya ga dabbobi da dama.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Mutane Uku Kan Zargin Sayen Motar Miliyan 75 Da “Fake Alert” Kano
Gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya halarci sallar jana’izar waɗanda abin ya shafa. A jawabin da aka karanto ta bakin mataimakinsa, Mani Malam Mummuni, gwamnan ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro a jihar.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta fara bincike kan jinkirin isowar jami’an tsaro bayan samun rahoton harin, tare da roƙon al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu.
A cewar wata sanarwa daga Ofishin Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Shehu Adamu Gusau, ’yan ta’addan sun kai harin ne sakamakon ƙin biyan harajin da suka ƙaƙaba wa mazauna ƙauyen.
Haka kuma, an sanar da kafa sansanin sojoji a Gwargwabe, domin hana sake aukuwar hare-hare, tare da kira ga al’umma da su ba jami’an tsaro haɗin kai.
Gwamnatin jihar ta ce ta tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa da buhunan hatsi 100, da kuma Naira miliyan 10 domin rage raɗaɗin da suka shiga.
Hakimin Nahuce, Alhaji Sulaiman Marafa, ya shaida wa Aminiya cewa mazauna yankin sun ƙi amincewa da biyan harajin da ake nema a kansu, suna mai cewa sun zaɓi tsayawa tsayin daka wajen kare ƙauyensu.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da aka kai yankin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka kashe a yankin zuwa bakwai cikin ɗan lokaci.
