News
Jami’an NDLEA Sun Kama Ɗan Kasuwar Da Ya Haɗiye Ƙunshi 95 Na Hodar Iblis 95 A Filin Jirgin Saman Kano
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wani ɗan kasuwa mai shekara 62, Nwabueze Nicholas Izueke, a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA), yayin da yake shirin tafiya China. An ce ya haɗiye ƙunshi 95 na hodar iblis mai nauyin kilo 1.589, waɗanda aka gano ta hanyar gwajin jiki kafin a tsare shi domin sa ido, inda ya kashinsu a sassa bakwai.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, wanda ake zargin ya ce ya shiga harkar ne domin samun kuɗin kammala gidansa a Iwollo, Jihar Enugu. An kama shi ne ranar 31 ga Janairu, 2026, yayin shirin tafiya Addis Ababa da jirgin Ethiopian Airlines.
Hukumar ta kuma ce ta kwato kilo 627.7 na wiwi a Kubwa, da Abuja, tare da daƙile yunƙurin safarar wasu kayan da aka ɓoye cikin lasifikar MP3 daga Enugu zuwa Abuja da Kaduna, inda aka kama wasu da ke da hannu a lamarin.
A jihohi daban-daban ciki har da Taraba, da Oyo, da Kwara, da Imo da Ondo, NDLEA ta kama mutane da dama tare da kwato hodar iblis, da tramadol, da pentazocine da sauran miyagun ƙwayoyi masu yawa. A Kwara ma, an gano kapsul 395,400 na tramadol da aka ɓoye a cikin tankar mai da ke kan hanyarta zuwa Maiduguri.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an hukumar kan nasarorin, yana mai umurtar su da su ci gaba da jajircewa a yaƙin rage safarar miyagun ƙwayoyi da wayar da kai a faɗin ƙasa.
