News
Dakarun Soji Sun Hallaka Ƴan Boko Haram 30 Tare Da Ƙwato Mutane 700 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Shalwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da kashe ƴan ta’adda 30 tare da ceto mutane 700 da aka yi garkuwa da su cikin mako guda, a wani ɓangare na tsaurara tsaro a Gabas ta tsakiya.
Wannan nasara ta samu ne ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai, kuma a cewar daraktan yaɗa labarai na shalkwatar tsaron Micheal Onoja an sami wannan ci gaba ne da haɗin gwiwar sauran sassan jami’an tsaro.
Himma Radio Ta Mayar Da Yara 80 Makaranta A Kano
Mr Onoja ya kuma ƙara da cewa bayan wani zaman bincike na sirri tare da gano maɓoyar mayaƙan Boko Haram da na ISWAP ne kuma aka afka musu.
A cewar sa, an ƙaddamar da wannan aiki ne a tsakanin garuruan Tumbuktu da Damboa, inda a nan aka kashe ƴan Boko Haram 20, ciki har da wani kwamanda mai suna Julaibib.
A ɓangaren yankunan Gwoza na Jihar Borno da kuma yankunan Hong da Mubi a jihar Adamawa ma, an mamayi yan ta’addar tare da hallaka da dama.
Bayanai sun nuna cewa yayin wannan samame an kuma kama wasu da ke yiwa mayaƙan safarar kayayyakin abinci da makamai da alburusai.
