News
Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Mahaƙar Ma’adinai A Filato Bayan Mutuwar Mutum 38
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe wata mahaƙar ma’adinai da ke Jihar Filato, bayan wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 38 sakamakon shaƙar iska mai guba.
Rahotanni sun nuna cewa masu haƙar ma’adinan sun rasa rayukansu ne bayan sun shaƙi iskar carbon monoxide da ta taru a cikin ramin da suke aiki a ciki. An ce iskar ta makale ne sakamakon fashewar wani bututu da ke dakon ta, lamarin da ya hana samun hanyar da za ta fita.
Kotu Ta Soke Belin Wanda Ake Zargi Da Lakadawa Wata Mata Duka A Kano
Haka kuma, wasu mutum tsakanin 25 zuwa 27 na ci gaba da karɓar magani a asibiti, bayan da suka samu raunuka da matsalolin numfashi sakamakon hatsarin.
Majiyoyi sun bayyana cewa galibin waɗanda abin ya rutsa da su matasa ne masu shekaru tsakanin 20 zuwa 35, abin da ya ƙara jefa al’ummomin yankin cikin alhini.
Jami’an tsaroJami’an tsaro sun killace wurin domin hana shiga da fita, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike don gano musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan iftila’i.
Mahukunta sun ce matakin rufe mahaƙar wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi domin ƙarfafa tsaro a fannin haƙar ma’adinai a Najeriya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
