Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Mahaƙar Ma’adinai A Filato Bayan Mutuwar Mutum 38

Published

on

Akalla Mutane 33 Sun Mutu A Wani Wurin Hakar Ma’adanai A Birnin Tehran

Gwamnatin Tarayya  ta bayar da umarnin rufe wata mahaƙar ma’adinai da ke Jihar Filato, bayan wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 38 sakamakon shaƙar iska mai guba.

Rahotanni sun nuna cewa masu haƙar ma’adinan sun rasa rayukansu ne bayan sun shaƙi iskar carbon monoxide da ta taru a cikin ramin da suke aiki a ciki. An ce iskar ta makale ne sakamakon fashewar wani bututu da ke dakon ta, lamarin da ya hana samun hanyar da za ta fita.

Kotu Ta Soke Belin Wanda Ake Zargi Da Lakadawa Wata Mata Duka A Kano 

Haka kuma, wasu mutum tsakanin 25 zuwa 27 na ci gaba da karɓar magani a asibiti, bayan da suka samu raunuka da matsalolin numfashi sakamakon hatsarin.

Majiyoyi sun bayyana cewa galibin waɗanda abin ya rutsa da su matasa ne masu shekaru tsakanin 20 zuwa 35, abin da ya ƙara jefa al’ummomin yankin cikin alhini.

Jami’an tsaroJami’an tsaro sun killace wurin domin hana shiga da fita, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike don gano musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan iftila’i.

Advertisement

Mahukunta sun ce matakin rufe mahaƙar wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi domin ƙarfafa tsaro a fannin haƙar ma’adinai a Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending