News
An Samu Ƙarancin Fitowar Masu Kaɗa Ƙuri’a A Zaɓen Cike Gurbi A Kano
An fara zaɓen cike gurbi na kujeru biyu a majalisar dokokin jihar Kano a safiyar Asabar, inda aka samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a sa’o’in farko na zaɓen.
Zaɓen na gudana ne a rumfunan zaɓe 1,014 da ke cikin mazabu 24, biyo bayan rasuwar Aminu Sa’ad Ungogo mai wakiltar Ungogo da kuma Sarki Aliyu na mazabar Kano Municipal a watan Disamban 2025.
WOFAN Ta Naɗa Dayyab Umar Mai Mai Rano a Sabon Matsayi Bayan Ritayarsa Daga Radio Kano
Kimanin masu rajista 535,000 ake sa ran za su halarci zaɓen. Rahotanni sun nuna cewa kayan zaɓe sun isa rumfunan zaɓe da wuri, amma jami’ai da mazauna yankuna sun nuna damuwa kan ƙarancin mahalarta, duk da fatan cewa yawan masu fitowa zai ƙaru yayin da rana ke tafiya.
Rahotanni daga sassa daban-daban na mazabun sun nuna cewa ana gudanar da zaɓen cikin lumana, ba tare da tangarda.
