News
WOFAN Ta Naɗa Dayyab Umar Mai Mai Rano a Sabon Matsayi Bayan Ritayarsa Daga Radio Kano
Ƙungiyar Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta naɗa tsohon Daraktan Sashen Labarai na Radio Kano, Dayyab Umar Mai Mai Rano, a matsayin mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai da ayyuka na musamman a matsayin mai aikin sa-kai, bayan ritayarsa daga aikin gwamnati.
Dayyab, wanda ya shafe fiye da shekaru ashirin yana aiki a fannin watsa labarai, ya shahara wajen gabatar da shirye-shirye da kuma hidimar Limancin a masallacin Juma’a da ke Rano.
Kano Ta Haska Domin Ramadan: Maltina Ta Kaddamar da Shirin “Light-Up” Don Ƙarfafa Haɗin Kan Al’umma
Naɗin nasa ya samu amincewar shugabanni da kwamitin gudanarwar WOFAN, bayan la’akari da rawar da ya taka tsawon shekaru 26 yana tallafa wa harkokin yaɗa labarai da inganta martabar ƙungiyar tun daga shekarar 2001.
A wani gajeren biki da aka gudanar ranar Juma’a 20 ga Fabrairu 2026 domin karɓar sabon aikinsa, ƙungiyar ta sanar da ba shi tallafin fara aiki domin kafa ofishinsa na kansa, tare da miƙa masa mota don sauƙaƙa zirga-zirgarsa wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora masa, kamar yadda SOLACEBASE ta ruwaito.
Da take jawabi a wajen taron, shugabar kwamitin zartarwa na WOFAN kuma jakadiyar zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya POLAC, Salamatu Garba, ta bayyana Dayyab a matsayin gogaggen ƙwararre da ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa hulɗar ƙungiyar da al’umma.
Ta ce zai yi aiki na sa-kai bisa tsarin biyan aiki gwargwadon yadda ya yi, na tsawon shekaru biyu a matakin farko, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa dabarun sadarwa da ƙara tasirin ayyukan WOFAN a tsakanin al’umma.
Shi ma shugaban kwamitin masu ba da shawara na fasaha na aikin WOFAN ICON 2, Sani Miko, ya yaba da sadaukarwar Dayyab tsawon shekaru, yana mai cewa yadda aka tsara masa rayuwa tun kafin ritaya na nuna hangen nesa da kulawar da ƙungiyar ke bai wa abokan aikinta.
Haka zalika, mamba na kwamitin gudanarwar WOFAN, Muhamud Daneji, ya ce ya fara sanin Dayyab ne ta muryarsa a shirye-shiryen Radio Kano, inda ya nuna ƙwarewa da bin ƙa’idojin aikin jarida.
A nasa bangaren, tsohon shugaban sashen aikin gona na Jami’ar Bayaro dake Kano, Muhammad Auwal Hussain, ya danganta nasarorin da Dayyab ya samu da jajircewa, riƙon amana da tsoron Allah.
Da yake karɓar takardar naɗinsa, Dayyab Umar Mai Mai Rano ya nuna matuƙar godiya ga Salamatu Garba, wadda ya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gabansa na ilimi da sana’a.
Ya bayyana cewa da taimakonta ne ya samu digiri da digiri na biyu, kuma a halin yanzu yana ci gaba da karatun digirin digirgir (PhD), yana mai jaddada kudurinsa na amfani da sabon matsayinsa wajen ƙarfafa ayyukan WOFAN da bunƙasa hulɗarta da al’umma.
