Connect with us

News

Sansanonin Amurka Za Su Fuskanci Luguden Wuta Muddin Ta Kawo Mana Hari — Iran

Published

on

FB IMG 1771630042587
Advertisements
ads

Iran ta bayar da sanarwar cewa dukkan sansanonin sojin Amurka, da wuraren ayyukanta da ke yankin Gabas ta Tsakiya za su fuskanci luguden wuta, idan har Amurka ta kai mata hari.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman Shugaba Donald Trump na cewa Iran tana da wa’adin kwanaki 10 zuwa 15 kacal don cimma yarjejeniyar nukiliya ko kuma ta fuskanci mummunan sakamako.

Ƴarinya ‘Yar Shekara 17 Ta Yi Garkuwa Kanta Tare Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Mahaifiyarta ‎ ‎

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya aika da wasika zuwa ga Sakatare Janar na Majalisar, inda ya bayyana cewa Iran ba ta son yaƙi, amma za ta kare kanta idan aka takale ta.

Iran ta gargadi ƙasashen Larabawa da ke karbar baƙuncin sansanonin Amurka, tana mai cewa dukkan sansanonin da ke kusa da ita za su iya fuskantar hari.

Sanarwar ta ambaci tsibirin Diego Garcia wanda ke ɗauke da sansanin Amurka da Birtaniya, a matsayin wurin da ka iya fuskantar hari.

Advertisement

A halin yanzu, Amurka ta girke manyan jiragen ruwan yaki guda biyu na USS Abraham Lincoln da USS Gerald R. Ford, tare da jiragen yaƙi masu lura da sararin samaniya a matsayin shirin ko-ta-kwana.

A daidai wannan lokacin, wasu jiragen yaƙin Rasha sun bi sahun Iran wajen gudanar da atisayen sojan ruwa a tekun Oman don nuna adawa da matsin lambar Amurka.

Wannan taƙaddama ta haddasa tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma hauhawar farashin zinare sakamakon fargabar ɓarkewar yaƙi a yankin.

 

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending