Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 15 A Yobe

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka akalla ‘yan ta’adda 15 tare da lalata wata cibiyar ajiya da ake zargin ana amfani da ita wajen kai hare-hare, a wani samame na musamman da aka kai a ƙaramar hukumar Gujba da ke jihar Yobe .

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa farmakin ya gudana ne a kusa da ƙauyen Lamusheri  da safiyar Lahadi, bayan makonni na tattara bayanan sirri da suka hada da hotunan tauraron dan adam da kuma sa ido ta sama.

Advertisement

An Gano Wani Kabarin Da Ya Haura Shekara 1,000 Cike Da Zinare A Panama

A cewar majiyoyin tsaro, an gano wurin ne a matsayin cibiyar da ake kaddamar da hare-hare tare da adana kayayyakin tallafawa ayyukan ‘yan ta’adda.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa dakarun soji tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force sun fuskanci turjiya yayin da suka kusanci wurin, inda ‘yan ta’addan suka bude musu wuta.

Sai dai sojojin sun yi dabarar kewaye maharan tare da katse hanyoyin tserewa. A rikicin da ya biyo baya, an kashe ‘yan ta’adda 15, yayin da wasu suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga.

Advertisement

An kuma kwato makamai da alburusai da dama, ciki har da jakunkunan ajiya na harsasai.

Rahoton ya ce sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga amma suna samun kulawar likitoci.

Advertisement

Jami’an tsaro sun ce duk da cewa yankin na cikin natsuwa a halin yanzu, ana ci gaba da sanya ido saboda yanayin tsaro na iya sauyawa a kowane lokaci. Sun kuma jaddada cewa kwarin gwiwar dakarun da ingancin aikinsu na nan daram.

 

Advertisement

PLATINUM

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending