Connect with us

News

An Gano Wani Kabarin Da Ya Haura Shekara 1,000 Cike Da Zinare A Panama

Published

on

panama tomb 768x512

Masana binciken tarihi sun gano wani tsohon kabari da ya haura shekaru 1,000 a ƙasar Panama, wanda ke ɗauke da gawawwakin mutane tare da kayan ado na zinariya da tukwane na yumɓu masu zane-zanen gargajiya.

An gano kabarin ne a wurin binciken tarihi na El Caño da ke yankin Natá, kimanin kilomita 200 kudu maso yammacin babban birnin ƙasar. Masana sun shafe fiye da shekaru 20 suna tono wurin, inda ake ci gaba da gano ragowar al’ummomin da suka rayu tun kafin zuwan Turawa.

Advertisement

An Gano Wani Kabarin Da Ya Haura Shekara 1,000 Cike Da Zinare A Panama

Jagorar binciken, Julia Mayo, ta bayyana cewa ƙasusuwan da aka gano suna kewaye da kayan zinariya da tukwane na gargajiya, abin da ke nuna cewa mutanen da aka binne a wurin na daga cikin masu matsayi mai girma a al’ummarsu.

Advertisement

Ta shaida wa AFP cewa an gina kabarin ne tsakanin shekarun 800 zuwa 1000 bayan haihuwar Almasihu.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin da aka binne a tsakiyar kabarin na sanye da kayan ado da dama, ciki har da awarwaron hannu guda biyu, ’yan kunne guda biyu, da kayan ado a ƙirji masu siffofin jemagu da kada — alamar matsayi da daraja a lokacin.

Advertisement

Bincike ya nuna cewa al’ummomin da suka rayu a yankin tsakiyar Panama tsakanin ƙarni na 8 zuwa na 11 ne suka yi amfani da wurin wajen binne mamatan su tsawon kusan shekaru 200. Tun da farko ma, an riga an gano wasu kaburbura guda tara makamancin wannan a wurin.

A cewar Ministry of Culture of Panama, wannan ganowa na da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar tarihin ƙasar da kuma al’ummomin da suka rayu a yankin tsakiyar Amurka kafin zuwan Turawa.

Advertisement

Masana sun ce binciken na kuma nuna cewa a wancan lokaci mutuwa ba ta nufin ƙarshen rayuwa ba, sai dai wata hanya ta sauyawa zuwa wani mataki, inda matsayi da darajar mutum ke ci gaba da kasancewa muhimmai har bayan mutuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending