Connect with us

News

ƘARFIN HALI: Wani Mutum Ya Kira ’Yan Sandan Kano Don Sanin Ko Sunansa Na Cikin Jerin Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Wani lamari mai ban mamaki ya faru a Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, bayan da wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ya kira domin tambayar ko sunansa na cikin jerin sunayen da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna mamaki kan yadda mutumin ya nemi wannan bayani kai tsaye.

Advertisement

Waye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton ‘Yansandan Najeriya

A cewarsa, mutumin ya kira shi ta waya yana son tabbatar da ko sunansa na cikin jerin sunayen da rundunar ke tattarawa na waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, bayan samun bayanan sirri daga jama’a.

Advertisement

“Ƙarfin hali! Wani ya kira ni yana tambaya ko sunansa na cikin masu safarar miyagun ƙwayoyin da ake kai rahoto a kansu,” in ji Kiyawa.

Sai dai kakakin rundunar bai bayyana ko sunan mutumin na cikin jerin ba, ko kuma ko ana bincikensa kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da rundunar ke ƙara tsaurara matakai kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin Jihar Kano, inda take karɓar bayanan sirri daga al’umma domin gano masu hannu a harkar.

Tun da farko, rundunar ta buƙaci mazauna jihar su rika miƙa bayanai cikin sirri kan mutanen da ake zargi da sayarwa ko rarraba miyagun ƙwayoyi a unguwanninsu.

Advertisement

A cewar Kiyawa, wannan tsari na da nufin rage shaye-shaye, safara da sauran laifukan da ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi domin inganta tsaro da lafiyar al’umma a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending