Connect with us

News

Kada Ku Takaita Suka Ga Gwamnatin Tarayya Kaɗai, Ku Sa Ido Kan Jihohi Da Ƙananan Hukumomi — Shugaba Tinubu 

Published

on

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci kafafen yada labarai su rika bibiyar yadda gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke tafiyar da kudaden da suke karba, ba gwamnatin tarayya kadai ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin da ya karbi bakuncin masu mallakar kafafen yada labarai da manyan editoci a fadarsa da ke Aso Rock a Abuja.

Advertisement

GOMAN KARSHEN RAMADAN: Dama Ta Ƙarshe Ga Mai Neman Rahamar Allah

Ya ce akwai bukatar kafafen yada labarai su fadada bincike da sa ido kan yadda ake amfani da kudaden gwamnati a matakan jihohi da kananan hukumomi, musamman bayan sauye-sauyen da suka bai wa kananan hukumomi damar karbar kudinsu kai tsaye.

Advertisement

Shugaban kasar ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar sun taimaka wajen kara kudaden shiga na jihohi, yana mai cewa a yanzu babu jihar da ke karbar bashi domin biyan albashin ma’aikata.

A cewarsa, karin kudaden da jihohi da kananan hukumomi ke samu ya samo asali ne daga karuwar samar da danyen mai, inganta tsarin tattara haraji, da kuma hukuncin Kotun Koli na shekarar 2024 da ya tabbatar da ‘yancin kananan hukumomi ta fuskar kudi.

Advertisement

Tinubu ya kuma gode wa kafafen yada labarai kan sukar da suke yi wa gwamnatinsa, yana mai cewa hakan na kara masa kwarin gwiwa wajen ci gaba da aiki.

Ya ce karanta jaridu a kowace safiya ya zama tamkar al’ada a gare shi, saboda hakan na taimaka masa wajen fahimtar yadda al’umma ke kallon tafiyar gwamnatinsa.

Advertisement

Dangane da cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi a shekarar 2023, Tinubu ya ce dole ne a dauki matakin domin kare tattalin arzikin kasar daga tabarbarewa.

Ya kara da cewa Najeriya na fara fita daga matsin tattalin arziki, yana danganta hakan da gyare-gyaren da aka yi a bangaren musayar kudaden waje da kuma kokarin da ake yi na dakile hauhawar farashin kayayyaki.

Advertisement

Shugaban ya kuma amince cewa kafafen yada labarai na fuskantar matsin tattalin arziki, amma ya yaba da hanyoyin da suke kirkira domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

 

Advertisement

 

Premier Radio 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending