Connect with us

News

Gobara Ta Ƙone Gidaje 3 A Kano

Published

on

Advertisements
ads

wata gobara da ta tashi a yankin Gaida da ke kusa da Fatima Bread a ƙaramar hukumar Kumbotso dake Jihar Kano, ta ƙone gidaje uku tare da lalata wasu kadarori, kamar yadda Hukumar Kashe Gobara ta jihar ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:05 na safe a ranar Talata, bayan sun samu kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin.

Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Hankali Kan Zaɓen 2027 Yanzu, Ya Manta Da Batun Tsaro Da Walwalar Jama’a  —Ndume

Sanarwar ta ce nan take aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar su da ke Sharada, tare da ƙarin jami’ai daga ofisoshin Sharada da Rijiyar Zaki domin shawo kan gobarar.

Hukumar ta bayyana cewa da isar jami’anta wurin, sun tarar da wani fili mai girman kusan kafa 50 zuwa 50, wanda ake amfani da shi wajen ajiye na’urar rarraba wutar lantarki (transformer), ya kama da wuta, abin da ya haddasa bazuwar gobarar zuwa gine-ginen da ke kusa.

Sai dai hukumar ta ce jami’anta sun samu nasarar dakile yaɗuwar wutar zuwa wasu gine-gine, tare da shawo kan gobarar.

Advertisement

Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga walƙiyar lantarki, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan lamarin.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending