News
Tirela Ta Murƙushe Matukin Babur
Wani matukin babur mai aikin kai saƙo ya mutu bayan wata tankar mai ta murƙushe shi a wani hatsarin mota da ya faru a titin Apapa–Oshodi Expressway, a yankin gadar Cele da ke jihar Lagos.
Hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Lagos (LASTMA) ta ce tankar mai ɗauke da dizal kirar HOWO mai lambar rajista RBC 38 XF ce ta buge babur ɗin da ƙarfi, lamarin da ya jefa matukin ƙarƙashin motar, inda ya rasu nan take.
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Mataimakin Gwamnan Kano Kan Dakatar Da Shirin Tsige Shi
A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Adebayo Taofiq, ya fitar, ya ce jami’an LASTMA sun isa wurin cikin gaggawa domin daidaita zirga-zirga da kuma hana aukuwar ƙarin haɗurra.
Rahotanni sun ce direban tankar ya tsere daga wurin bayan faruwar hatsarin, yayin da jami’an hukumar suka kwace motar domin ci gaba da bincike.
