News
Mutum 5 ‘Yan Gida Daya Sun Rasu A Hadarin Mota A Yobe
Akalla mutane biyar daga gida guda sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ranar Laraba a kan titin Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Yobe.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya shafi wasu mazauna ƙaramar hukumar Potiskum, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da jimami, sakamakon irin wannan babban rashi da aka yi.
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Mataimakin Gwamnan Kano Kan Dakatar Da Shirin Tsige Shi
Wani ɗan uwan mamatan, Dahiru Musa Talba, ya tabbatar da faruwar lamarin ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa dukkan waɗanda suka rasu ‘yan gida ɗaya ne. Ya ƙara da cewa wasu uku daga cikin dangin sun samu raunuka daban-daban a hatsarin.
A cewarsa, an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Damaturu, inda ake ci gaba da kula da lafiyarsu.
Da yake tabbatar da faruwar hatsarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da wasu suka jikkata. Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Jami’in ya ƙara da cewa hatsarin ya faru ne a kan titin Damaturu–Maiduguri, wanda aka sani da yawan zirga-zirgar ababen hawa.
An bayyana sunayen wasu daga cikin mamatan da suka haɗa da Hajjagana Dahiru Zayi, Ibrahim Dahiru Zayi, Muhammad Dahiru Zayi da Hauwa Dahiru Zayi, yayin da ake ci gaba da tantance sunan wani daga cikin ‘yan gidan.
