Connect with us

Politics

Ƙungiyar Mata Na ADC Sun Taya Kwankwaso Murna Kan Shiga Jam’iyyar

Published

on

ADC

Kungiyar Mata ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a fannin watsa labarai ta taya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauran manyan ‘yan siyasa murnar shiga jam’iyyar, tana mai bayyana matakin a matsayin wani ƙarin ƙarfi ga tafiyar dimokuraɗiyya a Najeriya.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Kodinetar kungiyar ta ƙasa, Hannatu Suleiman Abba, ta fitar, ta ce shigar Kwankwaso da sauran gogaggun shugabanni cikin ADC na nuna yunƙurin ƙarfafa shugabanci nagari da haɗin kai a fagen siyasa.

Advertisement

JIGAWA: Uba Ya Fasa Aurar Da ‘Yarsa Ga Wani Saurayi Saboda Goyon Bayan Tinubu

Kungiyar ta ce wannan mataki na da muhimmanci wajen faɗaɗa damar shiga harkokin siyasa ga ‘yan ƙasa, tare da ƙara wa jam’iyyar ƙarfi da tasiri a matakin ƙasa.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa, haɗuwar sabbin mambobi masu tasiri za ta taimaka wajen inganta manufofin jam’iyyar, musamman a bangaren adalci, daidaito da ci gaban al’umma.

Kungiyar Mata ta ADC a fannin watsa labarai ta kuma jaddada kudurinta na ƙara yawan shigar mata cikin siyasa, ta hanyar horaswa da wayar da kai, domin su taka rawa a matakai daban-daban na shugabanci.

Advertisement

Ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da tallafa wa manufofin da suka shafi kare muradun mata, matasa da marasa ƙarfi, tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar yaɗa sahihan bayanai a kafafen watsa labarai.

A ƙarshe, kungiyar ta taya Sanata Kwankwaso da sauran masu ruwa da tsaki murna, tare da yi musu fatan alheri a wannan sabuwar tafiya ta siyasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending