Uncategorized
Kano: Indabo Ta Bayyana Nasarorin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf, Ta Ce Babu Kwatankwacin Irinta a Najeriya
A Kano, mai bai wa gwamna shawara kan wayar da kai da haɗa kan al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa ta ƙaddamar da wani shiri na musamman da nufin haskaka ayyuka da nasarorin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da jama’a.
Indabo ta ce daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin ta samu akwai gyaran makarantu a faɗin jihar, da kuma ɗaukar nauyin karatun ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin bunƙasa ilimi.
Ta kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin kula da lafiyar mata masu juna biyu a dukkan ƙananan hukumomin Kano, a wani yunƙuri na rage mace-macen mata da jarirai tare da inganta kiwon lafiya.
A cewarta, an shirya wannan taro ne domin ƙara wayar da kan jama’a da kuma nuna goyon baya ga matakin rage kuɗin makarantu da gwamnatin ta aiwatar da kashi 50 cikin 100.
Indabo ta jaddada cewa a cewarta, “ba a taɓa samun gwamna mai tausayi da kula da jin daɗin al’umma kamar Abba Kabir Yusuf ba a Najeriya.”
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana cewa gwamnatin Yusuf ta aiwatar da ayyukan alheri da dama da ba za a iya ƙididdige su gaba ɗaya ba cikin ɗan lokaci kaɗan.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙara yawan ayyukan ci gaba domin tabbatar da Kano ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fice a Najeriya.
Shi ma a nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce gwamnatin na gudanar da ayyuka sama da 900 a halin yanzu a sassa daban-daban na jihar.
Ya jaddada cewa babu kamarta a ƙoƙarin da take yi wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Kano.
