News
Iran Ta Sake Rufe Mashigin Hormuz
Ƙasar Iran ta sake rufe mashigin ruwan Hormuz domin hana jiragen ruwa zirga zirga sakamkon ci gaba da hare haren da Isra’ila ke kai wa ƙasar Lebanon.
Wannan mataki ya biyo bayan matakin da Isra’ila ta ɗauka na ci gaba da kai munanan hare hare a Lebanon yau Laraba, wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane kusan 100.
Amurka Da Iran Sun Amince Da Tsagaita Wutar Kwanaki 14
Shirin tsagaita wutar da Pakistan ta jagoranci kullawa tsakanin Amurka da Iran ya ƙunshi dakatar da kai hare hare Lebanon, amma jim kaɗan bayan amincewa da yarjejeniyar sai firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar Lebanon bata ciki, kuma daga bisani shugaban Amurka Donald Trump ya goya masa baya.
Wannan mataki ya bai wa Isra’ila damar kai munanan hare haren da ta daɗe bata kai Lebanon ba, abinda ya haifar da kashe mutane kusan 100 da kuma lalata kadarorin jama’a.
Rahotanni sun ce tun bayan ɓarkewar yaƙin Isra’ila ta mamaye akalla kashi 14 na fadin ƙasar Lebanon, a hare haren da ta ce tana kai wa ne a kan mutanen Hezbollah dake goyan bayan Iran.
Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya zargi Isra’ilar ta ƙin aiwatar da buƙatun ƙasashen duniya na tsagaita wuta saboda hare haren da take ci gaba da kai wa.
Iran ta ce ci gaba da kai hare hare a Lebanon bijirewa yarjejeniyar da suka ƙulla da Iran ne, saboda haka ta dakatar da zirga zirgan jiragen ruwan da suka fara wucewa ta Hormuz, abinda ke nuna cewa akwai alamun koma baya dangane da cimma biyan buƙatar tsagaita wutar.
Ya zuwa yanzu dai ba a ji komai ba daga ƙasar Pakistan da ta jagoranci yarjejeniyar.
