News
Gwamnatin Tarayya Ta Tura Mutum 386 Gidan Yari Kan Laifukan Ta’addanci
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da daure mutum 386 daga cikin mutane 508 da ake tuhuma da aikata laifukan ta’addanci, bayan wata gagarumar shari’a da aka gudanar a Abuja.
Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.
Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Sunan Mutum 48 Da Ake Zargi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci
A cewarsa, an wanke mutum biyu daga zargin, yayin da aka sallami wasu takwas. Sauran mutum 112 kuma za a ci gaba da shari’arsu daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Yuni.
Rahotanni sun nuna cewa an fara wannan shari’a ne tun ranar Talata a Babbar Kotun Tarayya, inda aka yanke hukunci daban-daban ga wadanda aka samu da laifi, daga daurin shekaru takwas zuwa daurin rai-da-rai, bisa la’akari da girman laifukan da suka aikata.
Ministan ya ce matakin wani sako ne ga masu aikata laifuka, yana mai jaddada cewa Najeriya ba za ta amince da ta’addanci ba.
Ya kuma yabawa alkalai 10 da suka gudanar da shari’ar, duk da kasancewa lokacin hutun bukin Ista.
Kungiyoyi da suka hada da Nigerian Bar Association da Amnesty International sun halarci zaman kotun a matsayin masu sanya ido, domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Hukumomi sun ce wannan shari’a na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin magance matsalar tsaro da kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargi sun fuskanci shari’a cikin gaskiya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
