Connect with us

News

Mazauna Kaduna Na Koka Kan Karancin Ruwan Famfo Duk Da Kashe Naira Biliyan 16 

Published

on

FB IMG 1776032702242

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, mazauna na ci gaba da kokawa kan matsanancin karancin ruwan famfo, duk da kudade masu yawa da gwamnatin jihar ta ce ta kashe wajen gyaran manyan matatun ruwa.

Rahotanni daga sassa daban-daban na birnin Kaduna sun nuna cewa gidaje da dama sun shafe makonni, har ma watanni, ba tare da samun ruwa daga famfo ba. Lamarin da ya tilasta wa jama’a komawa sayen ruwa daga masu sana’ar sayar da shi a farashi mai tsada.

Advertisement

HARIN DAKARUN SOJIN SAMA: Mun Rufe Kasuwar Jilli Shekaru 5 Da Suka Wuce — Gwamnan  Borno

Wani mazaunin Unguwar Rimi ya shaida cewa, “Ba ma samun ruwa kwata-kwata a famfo. Dole sai mun saya domin biyan bukatun yau da kullum.” Haka kuma wani mazaunin Barnawa ya ce duk da kudaden da aka kashe, har yanzu ba su ga wani sauyi a zahiri ba.

Advertisement

Karancin ruwan ya haifar da karuwar kasuwancin sayar da ruwa. Sai dai masu sana’ar na cewa suna fuskantar kalubale wajen samo ruwan. Wani mai sana’ar, Nazir Musa, ya ce a yanzu ana sayar da kura mai dauke da jarkoki goma na lita 25 har Naira 2,000, farashin da ya yi tsada ga yawancin gidaje.

A bangaren gwamnati kuwa, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya ce kudaden da aka kashe wani bangare ne na shirin inganta tsarin samar da ruwa mai dorewa.

Advertisement

Ya kara da cewa an gyara manyan matatun ruwa guda shida tare da fadada hanyoyin rarraba ruwa zuwa gidaje, yana mai cewa ana samun karin samar da ruwa a hankali.

Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Uba Sani ta kuma ayyana dokar ta-baci a bangaren ruwa tun a shekarar 2023, domin shawo kan matsalolin da suka dade suna addabar bangaren.

Advertisement

Sai dai duk da wadannan matakai, mazauna sun ce har yanzu ruwa ba ya zuwa yadda ya kamata, abin da ke nuna cewa har yanzu akwai gibi a tsarin rarraba ruwan da kuma tasirin gyare-gyaren da aka yi.

Masana sun nuna cewa matsalar na da alaka da tsofaffin bututun ruwa, yawan malalar ruwa, rashin kulawa da kuma karuwar yawan jama’a—abubuwan da ke hana ruwan isa ga kowa.

Advertisement

Wani jami’in hukumar ruwa da ya nemi a sakaya sunansa ya amince da cewa ana fuskantar kalubale, amma ya ce ana sa ran ganin sauyi nan gaba.

Ya ce, “An yi aiki sosai wajen gyaran tsarin, kuma nan ba da jimawa ba jama’a za su fara ganin sakamako.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending